in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a alkinta hanyoyin ruwa da makamashi yadda ya kamata don raya Afirka
2018-09-05 10:14:38 cri

MDD ta yi kira da a yi kyakkyawan amfani da kafofin ruwa wajen samun makamashi, ta yadda za a sarrafa albarkatun da Allah ya horewa nahiyar wajen samun ci gaba mai dorewa.

Ofishin shirin samar da dauwamammen ci gaba na MDD(UNOSD) da hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin azrikin Afirka(ECA), da shirin kare muhalli na MDD da sashen MDD mai kula da harkokin tattalin arziki da jin dadin al'umma ne suka yi wannan kira yayin wani taron kwararru da masu tsara manufofi da suka hallara a birnin Addis Ababan kasar Habasha don tattauna matakai da yadda za a aiwatar da tsarin alkinta ruwa da makamashi don samun dauwamammen ci gaba a Afirka.

A jawabinsa, babban jami'i mai kula da harkokin muhalli a hukumar ECA Linus Mofor, ya ce, yanzu haka kasashen Afirka na dandana kudar tasirin matsalar canjin yanayi da yadda hakan ke shafar sassa da dama, ciki har da bangaren ruwa da makamashi da aikin gona.

A don haka ya kara jaddada bukatar bullo da managartan matakai game da karuwar bukatun makamashi da ruwa don inganta rayuwar al'umma da bunkasa tattalin arziki, da ma yadda za a magance karuwar matsin lamba kan albarkatun kasa sakamakon ci gaban birane da karuwar jama'a a nahiyar da ke fama da matsalar canjin yanayi.

Taron na kwanaki uku dai ya janyo mahalarta sama da 100 daga yankin Afirka, inda suka tattauna game da wasu muhimman alkaluma da yawan ruwa da makamashin da nahiyar ke fatan samu, ciki har da tsarin hade wasu sassa da kalubalen da ke da nasaba da ruwa da makamashi da matakan magance su da sauran batutuwa yayin da nahiyar ke kokarin samun ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China