Yau Talata ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu da ta Amurka sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, kasashen biyu sun tsai da kudurin dakatar da atisayen aikin soja wato UFG, wanda aka tsara gudanarwa a watan Agusta mai zuwa, domin tabbatar da wannan buri na raba zirin Koriya da makaman kare dangi, da kuma kafa tsarin shimfida zaman lafiya a zirin.
A dai wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya nuna maraba da wannan mataki, inda ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi cewa, ana fatan sassan biyu za su ci gaba sanya kokari, domin samun sabon ci gaba a fannin.(Jamila)