in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kociyan Kamaru ya bayyana shirinsa na tinkarar gasar AFCON 2019
2018-08-21 11:02:04 cri
Kociyan kungiyar wasan kwallon kafan jamhuriyar Kamaru Clarence Seedorf ya bayyana kudirinsa na horas da 'yan wasan tawagar kwallon kafan kasar don tinkarar gasar cin kofin kasashen Afrika (AFCON) a shekarar 2019.

"Muna da shirin da za mu gabatar da shi amma da farko dole ne mu hakikance ainihin abinda muke bukata. Za mu yi amfani da lokacinmu wajen kafa wata ingantacciyar kungiyar 'yan wasa wacce za ta wakilce mu a badi," Seedorf ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Yaounde. Wannan shi ne taron manema labaru na farko da ya gudanar tun bayan da ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru 4 da jamhuriyar Kamaru a farkon wannan watan. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China