in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar makomar da karfe da siminti za su gina wa Kenya
2018-08-20 14:21:55 cri

Bugu da kari, Lin Yihua ya ce, idan aka kwatanta da dabara ta gargajiya, watau a gina gine-gine a wurare kai tsaye, sabuwar dabarar da aka yi amfani da ita wajen gina sassan gine-gine a masana'anta, sa'an nan, aka hada su tare a wurin ta fi kyau, musamman ma a fannin kiyaye muhalli.

Haka zalika ya ce, a halin yanzu, bukatun al'ummomin kasar Kenya a fannonin gidaje da kuma gine-gine masu amfanawa al'umma ya wuce adadin da ake da su a kasar. Sabuwar dabarar da aka tsara wajen yin gine-gine ba ta bukatar lokaci mai tsawo, kuma tana da araha, lamarin da zai biya bukatun al'ummmomin kasar na halin yanzu yadda ya kamata.

Bugu da kari, a halin yanzu, kamfanin gine-ginen Wu Yi yana dukufa wajen ba da horo ga ma'aikatan kasar Kenya kan fasahohin gine-gine, ta yadda za su nemi ci gaba da kansu a wannan fanni. (Maryam)


1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China