in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar makomar da karfe da siminti za su gina wa Kenya
2018-08-20 14:21:55 cri

Bisa rahoton da bankin duniya ya fidda a shekarar 2017, adadin gidajen da hukumomin gidaje ta kasar Kenya suka samar bai kai dubu 50 ba cikin ko wace shekara, mutanen kasar kimanin miliyan 2 na fama da karancin gidaje, kana mutanen birane kimanin kashi 61 bisa dari suna zama cikin matsugunin masu fama da talauci. Amma bisa kididdigar da aka yi, cikin ko wace shekara, ana samun karin yawan al'ummomin dake zama a birane kimanin dubu dari 5, lamarin da zai haddasa karin matsala ta fuskar karancin gidaje a wannan kasa.

Yadda za a warware wannan matsala, ya janyo hankulan al'ummomi da shugabannin kasar Kenya, har ma da kamfanin gine-ginen kasar Sin wanda yake shiga aikin ginawar gidaje a kasar Kenya.

Bisa nazarin da kamfanin gine-ginen Wu Yi na kasar Sin dake kasar Kenya ya yi, an ce, bai dace a yi amfani da dabara ta gargajiya wajen gina gidaje a kasar Kenya ba. Mataimakin babban mananjan kamfanin Lin Yihua ya bayyana cewa, "Mun yi bincike a yankuna uku na kasar Kenya, wadanda suka hada da Nairobi, Mombasa da kuma Eldoret, inda muka gano cewa, hanyoyin dake cikin birane ba su da fadi, abun da ya sa ake rashin isassun wuraren da za a iya ajiye kayayyakin gine-gine. Haka kuma, zirga-zirgar siminti da kankare masu dimbin yawa zai bata muhallin biranen sosai."

Dangane da wannan lamari, kamfanin gine-ginen Wu Yi ya tsara wani sabon shirin gine-gine domin warware wannan matsala. A shekarar 2016, kamfanin ya zuba jari na dallar Amurka miliyan dari 1 domin gina masana'antar nazari da samar da kayayyakin gine-gine. Gaba daya fadin masana'antar ya kai muraba'in mita dubu 120, inda aka kafa yankunan samar da kayayyakin gine-gine guda shida. A shekarar 2017, yankunan shida suka fara aiki a hukunce, inda aka iya gina manyan sassan gine-gine da suka hada da babbar azara, ginshiki, banguna da dai sauransu cikin masana'antar, sa'an nan, aka yi jigilar su zuwa wurin, yayin da aka hada sassa daban daban tare bisa daftarin da aka yi, ta yadda za su kasance cikakken gini gaba daya.

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China