in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar DPRK ta yi kira ga Trump da ya nace ga manufar kyautata hulda tsakanin Amurka da DPRK
2018-08-19 16:04:06 cri

Jiya Asabar jaridar "Rodong Simun" ta kasar Koriya ta Arewa ta wallafa wani rahoto, inda aka yi kira ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya nace ga manufar kyautata huldar dake tsakanin kasarsa da kasar ta Koriya ta Arewa.

Rahoton ya bayyana cewa, al'ummun kasashen duniya sun yi farin ciki matuka da ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a kasar Singapore, tare kuma da fitar da hadaddiyar sanarwar, amma yanzu huldar dake tsakaninsu ta gamu da matsala, saboda wasu masu adawa da batun dake cikin Amurka suke matsa lamba ga kungiyar yin shawarwari tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa, har suke ta yada jita jitar cewa, Koriya ta Arewa tana da na'urorin samar da makaman nukiliya a asirce, a don haka aka bukaci Trump da ya dauki matakin da ya dace domin warware wannan matsalar da ta kunno kai.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China