in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DPRK ta yi allah wadai da sabon takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2018-08-10 10:59:58 cri

Koriya ta Arewa ta yi Allah-wadai da sabon takunkumin da Amurka ta kakaba mata, tana mai kira ga Amurkar da ta yi kokarin inganta alakar dake tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Koriya ta Arewa (KCNA) ya ruwaito mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa, Koriyar ta Arewar za ta ci gaba da martaba yarjejeniyar da shugaban Koriya ta Arewa da takwaransa na Amurka suka cimma yayin ganawarsu a kasar Singapore. Amma a gefe guda kuma sai ga shi Amurka ta kakaba mata takunkumi baya ga matsa lamba da take yi.

A farkon wannan watan ne, sashin baitul malin Amurka ya sanar da sanyawa wasu daidaikun mutane da wasu sassa uku na kasar takunkumi, ciki har da wani bankin kasuwancin kasar Rasha, bisa zarginsu ta hannu a shirin nukiliyar kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Koriyar ta Arewan ya ce, wannan mataki zai mayar da hannun agogon baya a kokarin da ake na aiwatar da sanarwar hadin gwiwar da kasashen biyu suka fitar, ciki kuwa har da kawar da makaman nukiliya, Haka kuma babu tabbas cewa, za a ci gaba da samun zaman lafiya a zirin na Koriya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China