in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Amurka za ta dandana kudarta idan ta tsananta takaddamar ciniki
2018-08-03 10:33:14 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya 2 ga wata a Singapore cewa, daidaita takaddamar ciniki tsakanin kasa da kasa ta hanyar amfani da dokar cikin gida, da kuma magance matsala ta hanyar daukar mataki na kashin kai, ya sabawa ka'idar kungiyar WTO, kuma hakan hanya ce mai cike da kuskure da ba ta dace da bunkasuwar zamani ba ko kadan. Baya ga kasancewar matakin ba zai haifar da cimma muradi ba, a hannu guda kuma zai sanya wadda ta dauki wannan mataki ta dandana kudar ta.

A yayin wani taron manema labarai bayan rufe taron ministoci na Sin da ASEAN a wannan rana, wani dan jarida ya tambayi Mista Wang game da ko Sin tana da nufin sake shawarwari da Amurka, bayan ta yi ikirarin cewa, za ta kara kakabawa Sin haraji na kashi 25 bisa dari kan kayayyakin da Sin za ta fitar zuwa Amurka, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 200. Game da hakan, Mista Wang ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana cikin zamani na dunkulewar duniya baki daya, kuma kasa da kasa na dogaro da juna ta hanyar hadin kai a fannoni daban-daban.

Ya ce kayayyakin da Sin take fitarwa Amurka, kashi 60 cikin dari kamfanonin ketare ne suke kerawa a kasar Sin ciki hadda kamfanonin Amurka, shin ko Amurka tana son bugawa kamfanoninta dake ketare haraji?Yawancin kayayyakin da Sin take fitarwa Amurka ba za a iya maye gurbinsu ba, kara kakabawa Sin haraji tamkar karawa jama'arta nauyi ne na zaman yau da kullum. Ban da wannan kuma, Amurka na yunkurin rage kayayyakin da take shigarwa daga kasar Sin ta hanyar kara buga kayayyakinta haraji, hakika dai za ta shigo da wadannan kayayyaki daga sauran kasashe, matakin da ba zai iya warware matsalarta na rashin samun daidaituwa a cikin cinikinta ba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China