in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban addini a Iran ya soke batun cimma yarjejeniya da Amurka
2018-08-14 10:17:44 cri

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya ce kasar ta Jamhuriyar Islama, ba za ta shiga sabuwar tattaunawa da Amurka ba.

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na website, Ayatollah Khamenei ya ba da misali da janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar da kasashen duniya suka cimma, yana mai cewa, Tehran ba za ta kuma zama a teburin sulhu da mayaudariyar gwamnatin ba.

Gidan talabijin na Press TV ya ruwaito jagoran na cewa, cikin sama da shekaru 40, Amurka ta yi ta bukatar hawa teburin tattaunawa sau da dama, sai dai ba ta samun abun da take so daga Iran.

Ya ce, yayin tattaunawa, alkawurra kawai da dadin baki Amurkawa ke yi, amma kuma suna son daya bangaren ya ba da kai, sannan ba sa amincewa da alkawurra.

Ya kuma jadadda cewa, a wannan lokaci da ake a yanzu, tattaunawa da Amurka ba ta haifarwa Iran wani alfanu ba.

Har ila yau, ya ce za su tattauna ne kadai idan Iran ta cimma karfin tattalin arziki da siyasa da take muradi, ta yadda matsin lamba daga Amurka ba zai yi mata illa ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China