in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rouhani ya bukaci Amurka ta ajiye manufofinta na kiyayya kan Iran
2017-05-23 10:52:28 cri

Shugaban kasar Iran da aka sake zabe Hassan Rouhani, ya bukaci Amurka ta ajiye manufofinta na kiyayya a kan kasarsa.

Da yake jawabi bayan lashe zaben shugaban kasar da ya yi, Hassan Rouhani ya ce, Iran da Amurka sun fuskanci matsaloli a dangantakarsu, kuma Amurka ta yi ta gazawa wajen aiwatar da munufofinta a kan Iran, ciki har da matsin lamba da kakaba takunkumi.

Ya ce, har kullum, Amurka kuskure take tafkawa a harin da take kai wa Afghanistan da Iraqi, haka zalika matsayarta a kan Syria da Yeman.

Ya kara da cewa, muddin ba za ta yi amfani da manufar cin moriyar juna tsakaninta da Iran ba, to Amurka za ta ci gaba da yin rashin nasara.

A jiya Litinin ne Rouhani ya ce, kasarsa za ta ci gaba da gwajin makamanta masu linzami muddin bukatar hakan ta taso, kuma ba za ta nemi izinin kowace kasa kafin yin gwajin ba.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China