A cewar Tjekero Tweya, Ministan kula da masana'antu da cinikayya da raya sana'o'i na Namibia, taron zai samar da wani dandali da masu kanana da matsakaitan sana'o'i za su baje kolin kayayyaki da hidimominsu.
Ya ce kamar yadda aka sani, dandali irin wannan, na ba kamfanonin dake sana'o'i daban-daban, damar baje sabbin kayayyakinsu da hidimomi, tare kuma da koyon wasu harkokin kasuwanci daga sauran kamfanoni, da nazarin yanayin da kasuwa ke ciki da kuma lalubo damarmakin kasuwanci.
A nasa bangaren, Mataimakin sakataren zartarwa na sashen tabbatar da hadin kan yankin, na kungiyar SADC, Thembinkosi Mhlongo, ya ce rayawa da sauya ayyukan samar da kayyyaki a yankin, na daya daga cikin muhimman abubuwan da kungiyar ta sanya gaba, cikin shirinta na manufofin ci gaba da aka yi wa gyara, na shekarar 2015 zuwa 2020, tare kuma da tsari da manufofin kungiyar na bunkasa ayyukan masana'antu. (Fa'iza Mustapha)