in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Somaliya sun kwace yankuna uku daga hannun mayakan al-Shabaab
2018-07-25 09:46:01 cri

Rundunar sojojin gwamnatin Somaliya (SNA) tare da masu tallafa musu sun zafafa kaddamar da hare hare domin fattatakar mayakan al-Shabaab a yankin kudancin kasar, sun ce sun yi nasarar kwace manyan yankuna uku daga hannun mayakan a kusa da tashar ruwa ta garin Kismayo.

Mukhtar Abdi Mohamed, shi ne babban kwamandan rundunar SNA a yankin, ya ce an hallaka biyu daga cikin mayakan na al-Shabaab da kuma raunata wasu mayakan uku a lokacin farmakin da sojojin suka kaddamar.

Mohamed ya ce, "Mun yi nasarar kwace yankuna uku, ciki har da yankin Arare wanda a baya yake karkashin ikon mayakan al-Shabaab".

Ya ce, sojojin suna kaddamar da farmakin ne da nufin kwato muhimman yankunan dake karkashin kungiyoyin 'yan ta'addan wadanda ke kaddamar da hare hare kan dakarun gwamnatin Somaliya a kullum, ya kara da cewa, za su ci gaba da aiki har zuwa lokacin da dakarun na SNA da na jihar Jubaland za su kwato dukkan yankunan daga hannun mayakan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China