in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNECA za ta shirya taron karawa juna sani game da cinikayya ta yanar gizo a Afrika
2018-05-23 10:39:16 cri

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (UNECA), ta jaddada muhimmancin dake tattare da wasu damammaki dake kunshe cikin tsarin cinikayya ta yanar gizo karkashin shirin yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci na kasashen Afrika (AfCFTA).

UNECA ta ce ta shirya wani babban taro mai taken "ciniki ta yanar gizo a Afrika" wanda ake sa ran gudanarwa a makon gobe.

Za'a gudanar taron daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni a helkwatar hukumar UNECA dake Addis Ababa, na kasar Habasha, ana sa ran za'a yi tattaunawa mai zurfi a tsakanin kwararrun masana game da batun cinikayya ta yanar gizo a Afrika.

A cewar MDD, tsarin cinikayya ta yanar gizo wata dama ce da za ta bude kofar samar da sabbin kasuwanni a bangarori daban daban, da suka shafi 'yan kasuwa da hajoji a Afrika, ana sa ran idan aka yi amfani da tsarin cinikayya ta yanar gizo, karfin jarin cinikayya a nahiyar zai iya kaiwa daga dala biliyan 50 zuwa dala biliyan 75 a duk shekara a cikin shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa.

Kungiyar tarayyar Afrika (AU), wadda ita ma ta daga matsayin tsarin ciniki ta yanar gizo da nufin bunkasa tsarin cinikayya, a shekarar da ta gabata ta kaddamar da wani tsarin ciniki ta intanet a Afrika, shi dai tsarin cinikin ta intanet zai ba da damar tallata hajoji, da ayyukan hidima da kuma samun bayanan da ake bukata game da cinikayya karkashin inuwar lema guda a duk fadin nahiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China