in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Hadaddiyar Daular Larabawa sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni
2018-07-20 22:00:04 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda a yanzu haka ke ziyara a Hadaddiyar Daular Larabawa, ya yi shawarwari tare da mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawan, kana firaministan kasar, Muhammad bin Rashid al Maktum, gami da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed Nahyan, inda suka kuduri aniyar kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni a tsakaninsu, da inganta hadin-gwiwarsu, da ciyar da huldodin kasashen biyu gaba zuwa sabon matsayi kuma daga bangarori daban-daban.

Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi Sin da Hadaddiyar Daular Larabawa su tabbatar da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da nunawa juna goyon-baya wajen neman samun bunkasuwa bisa tafarkin da ya dace. Kasar Sin na daukar Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin muhimmiyar kasa wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', da yabawa tunanin da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi ya bullo da shi na 'sake raya tsohuwar hanyar siliki'. Xi ya ce, ya zama dole kasashen biyu su kara yin mu'amala kan tsare-tsaren neman bunkasuwa da manufofin da suka shafi masana'antu, da aiwatar da wasu muhimman ayyuka na 'ziri daya da hanya daya', tare kuma da habaka tattalin arziki a yankin tekun fasha. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin na son zurfafa hadin-gwiwa tare da Hadaddiyar Daular Larabawa ta fannin makamashi daga dukkan fannoni, da inganta hadin-gwiwa a sauran fannonin da suka shafi zuba jari, hada-hadar kudi, da kirkire-kirkire. Har wa yau, ya kamata kasashen biyu su kara hadin-gwiwa a fannin tsaro, da kin amincewa da duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, kana firaministan kasar, Muhammad bin Rashid al Maktum cewa ya yi, kasarsa na fatan kara hadin-gwiwa da mu'amala da kasar Sin. A halin yanzu, Sin na samun dimbin goyon-baya daga kasashen duniya wajen jagorantar duniya don sake bunkasa hanyar siliki ta zamani da, kuma shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Hadaddiyar Daular Larabawa na son ci gaba da yin hadin-gwiwa da kasar Sin wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya'.

Shi ma a nasa bangaren, yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed Nahyan ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa haikan kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duk fadin duniya, ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da Sin take takawa a harkokin duniya. Yariman mai jiran gado ya ce kasarsa na fatan kara hadin-gwiwa da mu'amala da kasar Sin a fannonin neman bunkasuwa da yaki da ta'addanci da sauransu.

A wani labarin kuma, Sheikh Mohammed bin Zayed Nahyan ya karrama Xi Jinping da lambar yabo mafi daraja ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta Zayed, da baiwa Xi Jinping kyautar wani dokin Larabawa. Dokin Larabawa na daya daga cikin nau'o'in dawakai mafiya dogon tarihi da daraja a duk duniya, kuma masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa kan bayar da irin wannan doki kyauta ga baki mafi muhimmanci da daraja.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China