in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayanin Hotuna: Manufar Raya Lardin Zhejiang A Fannoni 8 Da Aka Gabatar Yau Shekaru 15 Ke Nan Ta Kawo "Almarar Zhejiang"
2018-07-17 21:18:07 cri

1: Taken hoto na farko: Manufar Raya Lardin Zhejiang A Fannoni 8 Da Aka Gabatar Yau Shekaru 15 Ke Nan Ta Kawo "Almarar Zhejiang"

Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da soma yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kuma ita ce shekarar cika shekaru 15 da sakatare-janar na JKS ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar raya lardin Zhejiang a fannoni 8. Lardin Zhejiang wanda yake kan gaba wajen soma yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, a kullum lardin yana kasancewa daya daga cikin lardunan da suka fi samun karfi da saurin bunkasuwar tattalin arziki a nan kasar Sin, tana ma kafa "almarar Zhejiang" dake jawo hankulan duk duniya. Yaya aka samu karfin kafa "almarar Zhejiang"?

2: Taken hotuna na biyu: Manufar Raya Lardin Zhejiang A Fannoni 8

A watan Yulin shekarar 2003, darektan kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na lardin Zhejiang na wancan lokaci Xi Jinping ya gabatar da manufar raya lardin a fannoni 8 ta hanyar amfani da albarkatun da lardin ke da su, ya gabatar da matakai 8 da ya kamata a dauka domin raya tattalin arzikin lardin nan gaba. Sabo da haka, an kira shirin da ya gabatar "Shiri Na 8+8".

1- Kara taka rawar nagartaccen tsarin da ake da shi a lardin Zhejiang wajen bunkasa tattalin arziki iri daban daban, musamman ma tsarin mallakar gwamnati, tare kuma da kara kyautata tsarin tattalin arzikin kasuwar gurguzu.

2- Kara taka rawar inda lardin Zhejiang yake wajen karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsa da birnin Shanghai da kuma lardin Jiangsu, ta yadda zai daga matsayinsa na bude kofa ga sauran wurare na gidan kasar Sin da kuma ketare.

3- Kara taka rawar sana'o'in da lardin Zhejiang take kwarewa domin hanzarta gina sansanonin kirkirre-kirkire tare kuma da raya masana'antun zamani a lardin.

4- Kara taka rawar daidaitaton ci gaban da aka samu a tsakanin garuruwa da yankunan karkara a lardin, domin kokarin cimma burin raya tattalin arziki da zaman al'umma a duk fadin lardin bai daya kamar yadda ya kamata.

5- Kara taka rawar kyakkyawan muhallin da lardin ke ciki, domin kokarin bunkasa lardin da ya zama "lardi maras gurbata muhalli".

6- Kara taka rawar albarkatun tsaunuka da ruwan teku da ake da su a lardin Zhejiang, domin raya tattalin arziki a yankunan dake bakin teku, musamman ma a yankunan dake fama da talauci, ta yadda za su iya zama sabon karfin ci gaban tattalin arzikin lardin Zhejiang baki daya.

7- Kara taka rawar kyakkyawan yanayin da ake ciki a lardin Zhejiang, domin samar da karin manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da karfafa ingiza a yi aikin bisa dokoki da lamuni da kuma kyautata aikin hukumomin gwamnatin lardin baki daya.

8- Kara taka rawar abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum da ake da su a lardin Zhejiang domin kokarin bunkasa lardin bisa ilmomin kimiyya da fasaha da kwararru, sannan a hanzarta raya ayyukan al'adu a fadin lardin.

Daga nan ne lardin na Zhejiang ya samu ci gaba cikin sauri, ayyuka a fannoni daban daban a lardin sun shiga wani sabon matsayi.

1  2  3  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China