in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta fara gwajin hakar danyen mai
2018-06-29 15:04:15 cri

A jiya ne kasar Habasha ta fara gwajin hakar gangan danyen mai, matakin da ake fatan zai kai ga farfado da tattalin arzikin kasar mai yawan al'umma kimanin miliyan 100.

Da yake jawabin yayin bikin kaddamar da aikin gwajin wanda rukunin kamfanonin kasar Sin na Poly-GCL zai gudanar a jihar Somali, ministan hakar ma'adinai, man fetur da iskar gas na kasar Meles Alemu, ya ce aikin hakar danyen man, wata babbar nasara ce bayan kwashe shekaru 100 da aka shafe ana kokarin hako mai a yankin ba tare da samun nasara ba.

Ya kara da cewa, hako man zai tabbatar da dorewar farfado da tattalin arzikin kasar, lamarin da zai canja matsayin kasar zuwa kasa mai ci gaban masana'antu dake samun matsakaicin kudin shiga nan da shekarar 2025. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China