in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha tana shata kan iyakokinta da sauran kasashe makwabta
2018-05-27 15:47:42 cri

Mahukuntan kasar Habasha sun sanar a jiya Asabar cewa, kasar tana shata kan iyakokinta da dukkannin kasashen dake makwabtaka da ita in ban da kasar Eritrea.

Shemsudin Ahmed, darakta mai kula da iyakokin kasar da albarkatun kasa karkashin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya ce, kasar Habashan tana aikin hadin gwiwa tare da kasashen dake makwabtaka da ita, domin tabbatar da shata kan iyakokin kasar cikin lumana da fahimtar juna, da kuma karfafa kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen, kamar yadda cibiyar yada labaran kasar Walta ta sanar.

Ya ce, shata iyakokin kasar zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, kuma zai ba da al'ummar kasar damar yin zirga zirga ba tare da wata tangarda ba.

Rikicin kan iyakoki tsakanin kasar Habasha da yankunan arewacin kasar dake makwabtaka da kasar Eritrea, ya hairfar da yaki da mummunan zubar da jini har na tsawon shekaru 2 tsakanin shekarar 1998 zuwa 2000, inda aka kiyasta rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 70,000 daga bangarorin biyu.

Tun daga wancan lokacin, kasashen biyu ba sa ga maciji da juna a sanadiyyar rikicin kan iyakokin kasashen biyu, lamarin da ke ci gaba da haifar da tashe tashen hankula lokaci bayan lokaci tsakanin sassan biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China