in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shigar kasar Sin cikin WTO ta amfanarwa yan kasuwar kasar Amurka
2017-07-12 13:15:42 cri
Wani bincike na baya bayan nan da kungiyar masana tattalin arziki ta kasar Amurka ta gabatar ya nuna cewa, iyalai Amurkawa da dama sun amfana matuka sakamakon shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO tun bayan shekarar 2001, a yayin da farashin kayayyakin masana'antu kamar rigunan sawa, da na'urorin lantarki da abinci ya ragu da kashi 7.6 cikin 100 tsakanin shekarun 2000 da 2006.

Wasu mansanan tattalin arziki su hudu daga kasashen Amurka, Sin da Australia sun bayyana a wata takardar da hukumar binciken alkaluman tattalin arziki (NBER) ta fitar a karshen watabn Yuni cewa, irin babban tasirin cigaban da kasar Sin ta haifar a duniya baki daya a bayyane yake, kuma fanni ne da ake cigaba da yin nazari kansa.

Bayanan binciken sun nuna cewa, tun lokacin da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO ta yi sanadiyyar saukar farashin kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa a Amurka da kashi 7.6 cikin 100, tsakanin shekarun 2000 da 2006. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China