in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da ministan tsaron kasar Amurka
2018-06-27 21:16:43 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da ministan tsaron kasar Amurka James N. Mattis a yau Laraba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin.

Yayin ganawarsu, shugaba Xi ya ce, duniyarmu na cikin wani yanayi na samun babban ci gaba, gami da babban sauyin tsare-tsarenta, inda bangarori daban daban, ke kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya, kana tattalin arziki na kokarin dunkulewa waje guda, don haka kasashen duniya na kara bukatar hadin gwiwa da juna.

A cewar shugaban, jama'ar kasar Sin na son raya kasarsu, ta yadda za ta zama wata kasa ta zamani mai bin hanyar gurguzu, sai dai ana daukar turbar raya kasa cikin zaman lafiya, maimakon dabarar neman habaka yanki da mulkin mallaka, ko kuma haifar da rudami a duniya.

Shugaban ya kara da cewa, huldar dake tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci matuka. Ya ce idan huldar dake tsakanin bangarorin 2 na da kyau, to, hakan zai haifar da moriya ga jama'ar kasashen 2, da ta kasashe daban daban, gami da taimakawa tabbatar da zaman lafiya, da walwala a duniyarmu.

A nasa bangaren, mista Mattis ya ce bangaren Amurka na dora cikakken muhimmanci kan huldar dake tsakanin sojojin kasashen 2. Kuma kasar Amurka na son kara musayar ra'ayi tare da kasar Sin, da habaka hadin gwiwar da ake yi tsakaninsu, da kokarin magance arangama da juna, ta yadda za a sanya huldar dake tsakanin sojojin kasashen 2, ta yadda za ta zama wani dalilin yaukaka dangantakar dake tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China