in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta kudu da madugun 'yan adawar kasar sun shiga tattaunawar sulhu a Khartoum
2018-06-26 10:49:03 cri

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit da jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar sun fara sabuwar tattaunawa a jiya Litinin a birnin Khartoum, a wani sabon yunkuri na warware rikicin siyasar kasarsu.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ne ya jagoranci tattaunawar wanda ta samu halartar shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Shugaba al-Bashir na Sudan ya sha alwashin samar da dukkan abubuwan da ake bukata wadanda za su taimaka wajen samun nasarar cimma matsayar warware rikicin siyasar da ya dabaibaye kamar Sudan ta kudun.

Mayardit, a bangarensa, ya jaddada aniyarsa ta yin dukkan abin da ya dace domin kawo karshen rikicin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China