in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin biyan kudin Sin zai shiga harkokin kasuwancin Kenya
2017-07-21 14:03:21 cri

Shugaban kamfanin Alibaba na kasar Sin, mai samar da dandalin biyan kudi ta kafar intanet Jack Ma, ya ce kamfanin na shirin shiga harkokin kasuwanci a kasar Kenya, inda zai samar da wani dandali na biyan kudi, ga kamfanoni dake aiki a kasar mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afrika.

Jack Ma wanda kuma ya kirkiro dandalin cinikayya ta intanet wato Alibaba, ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake gabatar da jawabi ga wani taron al'umma a jami'ar kasar Kenya.

Ma na ziyara ne a kasar, karkashin rangadin da cibiyar bunkasa harkokin cinikayya ta MDD UNCTAD ta shirya, domin bunkasa harkokin kasuwanci a duniya, tare da samar da abun koyi ga kanana 'yan kasuwa masu tasowa.

Taron wanda ya samu halartar ministan yada labarai na kasar Kenya Joe Mucheru da sakatare janar na cibiyar bunkasa harkokin cinikayya ta MDD Mukhisa Kituyi ya bayyana wasu dabarun kasuwanci da cinikayya ta intanet.

A jawabinsa, mashahurin 'dan kasuwar na kasar Sin ya bukaci 'yan kasuwa da masu kirkire-kirkire su rungumi faduwa da rashin nasara a matsayin abun da zai yi kyakkyawan tasiri ga burinsu na kasuwanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China