in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Ziyarar da Putin zai yi a Sin tana da babbar ma'ana
2018-06-04 13:11:11 cri

Babban jami'in diplomasiyyar kasar Sin Wang Yi ya sanar a jiya Lahadi cewa, ziyarar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kai kasar Sin tana da matukar amfani a kokarin da ake na daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Rasha.

Mamba a majalisar gudanarwar kasar ta Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi wannan tsokaci ne a yayin da yake ganawa da takwaransa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, a gefen taron ministocin kasashen waje na kungiyar kasashen mambobin BRICS.

Wang ya ce, ziyarar za ta kasance irinta ta farko da shugaba Putin zai kai kasar Sin a sabon wa'adin shugabancinsa, kuma ita ce ta farko da shugaba Xi Jinping da Putin za su gana da juna a cikin wannan shekara, wanda ta kasance ziyara mai matukar muhimmanci ta fuskar karfafa dangantaka da kuma daga matsayin alakar dake tsakanin Sin da Rasha zuwa mataki na gaba.

Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Rasha domin tabbatar da ganin an cimma nasarori masu yawa a yayin ziyarar, da kuma bunkasuwar dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangaren, Lavrov ya ce, kasar Rasha tana daukar ziyarar da Putin zai kai kasar Sin da muhimmanci.

Ya kara da cewa, Rasha ta gamsu da irin shirye shiryen da ake yi game da ziyarar da shugaban kasarsa zai kai a kasar Sin, kuma a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin domin tabbatar da ganin an cimma nasarorin da ake fata dangane da ziyarar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China