Wang Xiaohong, mataimakin shugaban hukumar 'yan sandan kasar Sin, ya yi furucin ne, a jiya Alhamis, a wajen taron shugabannin 'yan sandan duniya karo na 2 na MDD, wanda ke gudanar a hedkwatar majalissar dake birnin New York.
Jami'in na kasar Sin ya ce, kasarsa za ta kara zuba ma aikin kiyaye zaman lafiya jari, da gudanar da kwas na horar da ma'aikata, da tura kwararru masu horaswa bisa hadin gwiwa da MDD. Kana, a cewarsa, za a bada muhimmanci ga shirin horar da ma'aikata a nahiyar Afirka, don cimma burin da aka sanya na horar da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya 1000. Ya ce, a shirye kasar Sin take, wajen kokarin taimakawa kasashen Afirka karfafa ayyukan tsaro da shari'a, karkashin tsare-tsaren da MDD ta tanada. (Bello Wang)