in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na Senegal
2018-06-21 13:15:26 cri
Jiya Laraba, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Senegal Sidiki Kaba, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a Sin.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya bayyana cewa, a wata mai zuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai je kasar Afirka ta Kudu domin halartar taron ganawar shugabannin kasashen BRICS, yayin da kai ziyarar aiki a kasashen Afirka, lamarin da ya nuna cewa, Sin na mai da hankali kwarai da gaske kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. A halin yanzu kuma, Sin da Afirka suna shirye shiryen gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da za a yi a watan Satumba a birnin Beijing. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Senegal da ma sauran kasashen Afirka wajen gudanar da taron yadda ya kamata, ta yadda zai kasance babban taro na karfafa dunkulewar Sin da kasashen Afirka.

A nasa bangaren, Mr. Kaba ya ce, kasarsa tana mai da hankali sosai wajen raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Senegal, tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, yayin da ba da karin gudummawa kan gina taron dandalin tattaunawar dake tsakanin Sin da Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China