in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal ta doke Poland a gasar cin kofin duniya
2018-06-20 13:28:32 cri

A daren ranar Talata bisa agogon kasar Rasha, an gudanar da wasa na biyu a rukunin H a gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa, inda kungiyar wasan kwallon kafan Senegal ta doke ta kasar Poland da ci 2 da 1, hakan ya sa Senegal ta zama kungiyar wasa ta farko daga nahiyar Afirka data samu nasara a gasar cin kofin duniya dake gudana a kasar Rasha.

Gasar cin kofin duniya ta wannan karo cike take da ban mamaki. A daren jiya Talata, bayan da kungiyar wasan Japan ta doke takwararta ta kasar Columbia, kungiyar Senegal ma ta doke kungiyar Poland da ci 2 da 1. Wasu mintuna 37 bayan da aka kaddamar da wasa a tsakanin Senegal da Poland, Idrissa Gueye na Senegal ya buga kwallo a wurin da ya yi kusa da ragar kunigyar Poland, inda kwallon ya ci karo da kafar Cionek, sa'an nan ya karkata hanya ya shiga cikin ragar Poland. Daga bisani a minti na 60, Grzegorz Krychowiak na Poland ya mika kwallo ga abokan kungiyarsa dake baya, amma ya yi kuskure, inda M'Baye Niang na Senegal ya saci kwallon, ya kuma kutsa kai cikin gidan Poland, tare da samun maki. Zuwa minti 86 na gasar, Krychowiak ya samu damar gyaran kuskuren da ya yi a baya, inda ya shigar da kwallo da kai cikin gidan Senegal. Sai dai bai samu damar daidaita yanayin da kungiyarsa ke ciki ba. Duk da cewa masu sha'awar wasan kwallon kafa sun nuna kyakkyawan fatansu na ganin kungiyar Poland ta zama kan gaba a rukunin H, amma a wajen gasar da ta buga da Senegal jiya, 'yan wasan Poland basu nuna kwarewarsu ba, inda suka yi kurakurai da yawa a fannin tsaron gida, kana dan wasan gaba Lewandowsk shi kadai ne ke kokarin neman damar samun maki amma ya gagara. Musamman ma ta la'akari da kwallayen biyu da aka buga cikin ragar Poland, wadanda daya shi ne yadda 'yan wasan Poland suka ci gidan kansu, yayin da dayan ma aka buga cikin ragar Poland ne ba tare da fuskantar masu tsaron gida ba, lamarin da ya sanya masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Poland takaici matuka.

Bayan gasar, mai horar da 'yan wasan kungiyar Poland Adam Nawalka ya gayawa wakilin CRI cewa,

"Kafin gasar mun yi nazari kan halayyar kungiyar Senegal, mun san 'yan wasan kungiyar suna iya gudu, kuma suna da kwarewa a fannin sarrafa kwallo, amma duk da haka sakamakon gasar yana da ban mamaki. Ba na son kara yin bayani kan hasarar da muka samu, zamu nemi daidaita kuskuren a gasa mai zuwa."

Kungiyar Senegal ta samu damar koma gasar cin kofin duniya bayan wasu shekaru 16. Cikin gasar da aka buga a jiya Talata, 'yan wasan Senegal sun nuna kwarewarsu a fannin gudu da kuma kai hari, kuma sun yi amfani da damar da 'yan wasan Poland suka ba su na yin kuskure yayin mika kwallo, ta yadda suka samu maki. Babban kocin kungiyar Senegal Aliou Cisse, shi ne kyaftin din kungiyar Senegal da ta shiga zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta Japan da Koriya ta Kudu wasu shekaru 16 da suka wuce. Game da nasarar da kungiyarsa ta samu, Cisse ya bayyana cewa,

"Hakika dukkan masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Senegal suna goyon bayanmu, har ma, za mu iya cewa daukacin nahiyar Afirka suna rufa mana baya. Muna alfahari sosai ganin yadda muke taka kwallo a madadin kasarmu, kuma za mu ci gaba da samun nasara."

Dan wasan gaba mai lamba 19 na kungiyar Senegal Niang ya samar da gudunmowa a dukkan kwallen 2 da aka buga cikin ragar Poland jiya. Dan wasan mai shekaru 24 a duniya yana taka kwallo a kulob din Turin na kasar Italiya, hakika 'yan wasan 22 daga cikin kungiyar Senegal suna buga kwallo a kasashen Turai. Niang ya bayyana dalilin da ya sa suka samu nasara a gasar, inda ya ce,

"Muna son nuna fasahohinmu, saboda haka mun yi mako guda muna kokarin share fagen gasar. Daga bisani sai muka yi amfani da dabarar da muka tsara ke nan."

A ranar Lahadi 24 mai zuwa, kungiyar Senegal zata kara da kungiyar Japan, wadanda zasu wakilci kungiyoyi na nahiyoyin Afirka da Asiya wajen gudanar da gasar. Ko wanene daga cikinsu zai samu nasara? Bari mu zura ido mu gani. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China