180524-capoeira-wani-wasan-da-ya-hada-fasahar-fada-da-ta-rawa-bello.m4a
|
Wasan Capoeira ya fara gama gari tsakanin bayi 'yan Afirka ne lokacin da sojojin kasar Netherland suka kai hari ga yankin Brazil tsakanin shekarar 1624 zuwa ta 1630. A lokacin bayi da yawa sun tsira daga gandun noma da aka ajiye su, suka shiga cikin kungurmin daji, inda suka kafa wasu kauyuka, suka zama mutane masu 'yanci a can. Domin tinkarar hare-haren da 'yan mulkin mallaka na Portugal suka dinga kai musu, jama'ar da suka zauna a cikin wadannan kauyukan da aka kafa cikin daji sun yi kokarin koyon fasahar Capoeira. Ta wannan hanya sun samu damar kyautata fasahar wasan fadan, inda ya fara zama wata fasahar fada mai karfi.
Bayan da aka 'yantar da bayin kasar Brazil a shekarar 1888, wasu bayin da suka samu 'yanci sun shiga cikin manyan biranen kasar, tare da fasaharsu ta Capoeira. Sai dai wasunsu sun shiga gungun 'yan baragurbi, da yin amfani da Capoeira wajen aikata laifi, lamarin da ya sa aka dade ana hana koyon fasahar Capoeira, har zuwa shekarun 1930, lokacin da aka fara kallon Capoeira a matsayin wani wasa na motsa jiki.(Bello Wang)