Dan wasan bayan Chelsea Gary Cahill, shi ne ya fara zarawa kungiyar wasan Three Lions kwallo yayin da ya buga kwallon wanda ya mayarta gida yayin da Kieran Trippier ya yi bugu daga kusurwa mintoci uku da fara wasan.
Kaftin din Ingila Harry Kane ya yi wani bugu inda ta wuce mai tsaron ragar Najeriya Francis Uzoho, kafin tafiya hutun rabin lokaci bayan da ya karbi kwallon daga wajen Raheem Sterling.
Shi kuwa Dele Alli shi ne ya zarawa Najeriyar kwallo. Dan wasan wanda aka haifa a kasar Birtaniya, yana da damar wakiltar kungiyar wasan Super Eagles, kasancewar mahaifinsa dan Najeriya ne.
Dan wasan Arsenal Alex Iwobi shi ne ya mayar da wasan ya koma ci 2-1 cikin mintoci 2 bayan da ya buga kwallon gida yayin da Odion Ighalo ya buge kwallon.
Ingila zata karbi bakuncin costa Rica a ranar 7 ga watan Yuni gabanin tafiya Rasha, inda zasu bude wasansu na gasar cin kofin duniyar, inda zasu buga wasan da Tunisiya a rukunin G a ranar 18 ga watan Yuni.
A rukunin D, Najeriya zata buga wasanta na farko a ranar 16 ga watan Yuni.(Ahmad Fagam)