in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 46 sun mutu bayan da kwale kwale ya kife a tekun Tunisia
2018-06-04 11:07:44 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Tunisiya ta ce, adadin bakin haure ta barauniyar hanya da suka mutu a sanadiyyar kifewar kwale kwale a tekun kudu maso gabashin Tunisiya ya tasamma 46.

Rachid Bouhawala, jami'in yada labarai na ma'aikatar tsaron kasar Tunisiya ya ce, kawo yanzu mutunen da ake ceto sun kai 75, wadanda suka hada da 'yan asalin kasar Tunisiyan 60, da wasu mutanen 5 daga kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika, mutane 2 daga kasar Morocco, sai mutum guda daga kasar Libya.

Ana cigaba da gudanar da aikin ceto bisa hadin gwiwar dakarun sojoji, da ma'aikatan hukumar tsaron teku da jami'an tsaro na fararen kaya.

Baki daya bakin haure ta barauniyar hanyar su 180 ne suke cikin kwale kwalen, wadanda suka hau daga tsibirin Kerkennah dake tekun kudu maso gabashin kasar ta Tunisiya, daga cikinsu akwai 'yan Afrika 80.

Tsibirin na Kerkennah ya yi kaurin suna a matsayin babbar hanyar da bakin haure ta barauniyar hanya ke tsallakawa zuwa kasashen Turai daga kasar Tunisya. Daga farkon wannan shekara, kimanin bakin hauren 1,910 ne daga Tunisiya suka tsallaka tekun kasar Italiya, kamar yadda hukumar sanya ido kan bakin haure ta kasa da kasa ta tabbatar.

Wasu alkaluman binciken da dandalin tattalin arziki da hakkin dan adam na kasar Tunisiya ya fitar ya nuna cewa, kimanin 'yan kasar Tunisiyan 9,329 ne suka yi yunkurin tsallakawa tekun Meditereniya a shekarar 2017, yayin da dakarun tsaron tekun Tunisiya suka hana tsallakawarsu kashi 34 bisa 100 daga cikinsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China