in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da taimakawa tattalin arziki da ci gaban Tunisia
2018-05-25 10:29:50 cri

Sabon jakadan kasar Sin a Tunisia Wang Wenbin, ya ce kasar Sin za ta zurfafa hadin gwiwa da inganta kawance tsakaninta da kasar dake arewacin Afrika.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana haka yayin bikin mika wa shugaban Tunisia, Beji Caid Essebsi shaidarsa ta wakiltar kasar Sin, ya kara da cewa, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa tattalin arziki da ci gaban Tunisia.

Jakadan ya jadadda cewa, taron kolin dandalin tattaunawa na kasar Sin da nahiyar Afrika, da zai gudana a watan Satumban bana a birnin Beijing, zai ba da sabbin damarmaki ga raya huldar dake tsakanin sassan biyu.

A nasa bangaren, shugaban Tunisia, Beji Caid Essebsi, ya ce a shirye kasarsa take, ta hada hannu da kasar Sin wajen kyautata huldar dake tsakaninsu.

Ya kuma godewa Sin bisa taimakon da ta dade tana ba kasarsa, yana mai fatan za ta ci gaba da ba da taimakon ga tattalin arziki da sauye-sauye da ci gaban kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China