in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun mutu a sakamakon fashewar boma-bomai a babban birnin kasar Tunisiya
2015-11-25 10:14:27 cri

Kafofin watsa labaru na kasar Tunisiya sun bayyana cewa, wasu boma-bomai da aka dasa cikin wata mota sun tarwatse a Tunis fadar mulkin kasar Tunisiya. Lamarin wanda ya auku a yammacin jiya Talata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, a yayin da kuma wasu mutane 20 suka ji raunika.

Bayan aukuwar lamarin, shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya soke shirin kai ziyara a kasar Switzerland, kuma ya yi jawabi ta kafar talibijin da daren wannan rana, yana mai cewa lamarin wani hari ne na ta'addanci. Daga nan sai ya sanar da sake kaddamar da dokar ta baci a kasar ta tsahon wata daya.

Da fari dai an kafa dokar ta baci ta hana zirga-zirgar jama'a daga karfe 9 na dare zuwa karfe 5 na safiya ranar Laraba a birnin na Tunis.

A ranar 18 ga watan Maris na wannan shekara ma dai an kaddamar da hare-hare tare da yi garkuwa da mutane, a wani dakin nune-nune na birnin Tunis, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23. A kuma ranar 26 ga watan Yuni, an kai hari a wani dakin cin abinci dake birnin Sousse dake bakin teku, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 38.

Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren. A farkon watan Yuli, an kaddamar da dokar ta baci a kasar Tunisiya, kafin daga bisani a soke ta a farkon watan Oktoba. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China