in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan ganawar shugaba Trump da Kim
2018-05-24 11:04:56 cri

Mamba a majalissar zartaswar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasar sa na matukar goyon bayan tattaunawar da ake fatan shugaban Amurka Donald Trump zai yi da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Wang Yi ya ce, ganawar kai tsaye tsakanin shugabannin biyu, za ta zamo wani ginshiki na warware batun nukiliya a zirin Koriya. Wang ya yi tsokacin ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo bayan ganawar jami'an biyu.

Ya ce, Sin na da imanin cewa, shugaba Trump da shugaba Kim na da iko, da kwarewar aiki, wadda za ta ba su damar daukar matakai da suka dace, domin wanzar da zaman lafiya a zirin Koriya, tare da sada dukkanin duniya da kyakkyawan labara.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China