in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump da Moon sun amince su warware rikicin zirin Koriya cikin ruwan sanyi
2017-11-08 10:39:48 cri

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in, sun amince su warware rikicin zirin Koriya cikin ruwan sanyi, tare da cimma yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashensu.

Yayin wani taron manema labarai bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi jiya Talata a fadar shugaban kasar Koriya ta Kudu, shugaba Moon ya ce, sun amince su warware batun nukiliyar zirin Koriya cikin ruwan sanyi, tare da samar da dawwamammiyar maslaha.

A nasa bangaren, shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ba ya fatan yin amfani da karfi a kan Koriya ta Arewa, yana mai bukatar kasar ta koma teburin sulhu, tare da cimma maslahar da za ta amfane ta da duniya baki daya.

Sai dai, Donald Trump ya ki cewa, komai dangane da tambayar da aka masa kan ko zai amince da tattaunawa ta kai tsaye idan Koriya ta Arewa ta bukata.

A jiya da rana ne shugaba Trump ya isa Koriya ta Kudu a ziyarar da yake a nahiyar Asiya, inda ya kai ziyara sansanin sojin Amurka na Humphreys da aka yi wa kwaskwarima a baya bayan nan, wanda ke da nisan kilomita 40 daga kudancin birnin Seoul. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China