Ma'aikatar harkokin wajen Habasha, ta ce zargin kasar da Eritrea ta yi na mara baya ga 'yan tawayen Eritrean, ba shi da tushe.
A ranar Laraba da ta gabata ne, ministan labarai na Eritrea, ya fitar da sanarwar da ta zargi makwabtan kasashen, da suka hada da Sudan da Habasha, da hada baki don taimakawa kungiyoyin 'yan tawaye dake kasar.
Sanarwar ta Eritrea, ta kuma ce Habasha da Sudan, sun amince su tura 'yan tawayen na Eritrea zuwa kan iyakokinsu da kasar, domin saukaka musu kai hari kasar da tsarewa.
Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Habasha Meles Alem, ya ce zargin na Eritrea karya ne tsagwaronta.
Ya kuma ce, har yanzu, Habasha na kan bakanta na tattaunawa da sulhuntawa da Eritrea ba tare da sharadi ba, duk kuwa da takkadamar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)