in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in kasar Sin: Tsarin harajin da Amurka ta dorawa Sin ya ci karo da alkawarin da ta dauka
2018-03-27 10:50:21 cri
Wakilin kasar Sin a hukumar ciniki ta duniya WTO Zhang Xiangchen ya ce, matakin baya bayan nan da kasar Amurka ta dauka game da kara kudaden haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa Amurka ya ci karo da alkawarin da ta dauka kuma matakin ya kamata ya kasance karkashin ka'idojojin yarjejeniyar warware sabani ta DSB dake karkashin hukumar ciniki ta duniya.

Zhang ya ce, abin da Amurka ta yi ya saba da ka'idojin hukumar WTO, wanda ta amince da shi sama da shekaru 10 da suka gabata, kuma Amurka ta fito fili karara ta yi gaban kanta karkashin sashen doka ta 301, matakin da reshen hukumar DSB ne kadai yake da alhakin aiwatarwa.

Sashen doka na 301 wani ma'auni ne dake karkashin tsarin dokar ciniki ta Amurka wadda ta kafa a shekarar 1974, wanda ya baiwa shugaban kasar damar daukar dukkan matakan da yake ganin sun dace, ciki har da batun daukar fansa, idan har an gudanar da bincike dake nuna cewa wani nau'in ciniki na kasahen waje ya illata moriyar kasar, ko kuma ya takaitawa Amurka wasu harkokin cinikayyarta, ko kuma yin abu ba bisa ka'ida ba, ko kuma nuna banbanci.

A bisa tsarin dokar WTO da yarjejeniyar Amurka, kasar ta Amurka ba ta da ikon daukar wani mataki na kashin kanta ta hanyar la'akari da tsarin dokar ta 301, idan har ta gudanar da bincike wanda ya nuna cewa wata kasa ta saba da yarjejeniyar dokar ta WTO, Zhang ya furta hakan ne a lokacin taron majalisar WTO game da batun cinikayya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China