Cikin wata sanarwa da ya aike ga taron kwamitin tsara manufofi na asusun bada lamuni na duniya IMF, Roberto Azevedo, ya ce hadin kan duniya na da muhimmanci wajen saukaka takkadama da kare ci gaban da aka samu kawo yanzu.
Ya ce kungiyar WTO da aka kirkiro a matsayin wani dandali da mambobinta za su tallafawa juna, za ta taka rawa yadda ya kamata a wannan fannin.
Ya yi gargadin cewa, tabarbarewar huldar cinikayya tsakanin manyan kasashe za ta yi illa ga ci gaban da ake gani a baya bayan nan.
Darakta Janar din ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su ci gaba da karfafa hadin kai kan batutuwan da suka shafi cinikayya ta hannun WTO, yana mai cewa zai taka muhimmiyar rawa wajen kare ta'azzarar takkadamar cinikayya da ake ciki yanzu, da kuma mara baya ga ci gaba da samar da guraben ayyukan yi a duniya. (Fa'iza Msutapha)