Lu Kang ya bayyana cewa, a ganin kasar Sin, kudurin da Koriya ta Arewa ta yanke, zai taimaka wajen sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya, da sa kaimi ga warware batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya da matsalar zirin Koriya ta hanyar siyasa.
Cimma burin kau da makaman nukiliya da samun zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya ya dace da moriyar zirin Koriya da jama'ar dake yankin, har ma da sauran kasashen duniya.
Lu Kang yana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su cimma daidaito, tare da daukar matamai don yin kokarin cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa da ci gaba a yankin, ya na mai cewa Kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan batun. (Zainab)