in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu kasar Sin na matsayin kasa mai tasowa mafi girma
2018-04-16 09:19:01 cri

Wani masani kan harkokin tattalin arziki na cibiyar ba da bayanai game da harkokin tattalin arzikin kasar Sin Wang Yuanhong, ya ce duk da nasarorin da ta samu ta fuskar tattalin arziki, har yanzu kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya.

Wang Yuanhong ya ce, har yanzu kudin shigar kowanne 'dan kasar ya yi kadan, baya ga gibin dake tsakanin birane da kauyuka da kuma rashin karfin takara ta fuskar masana'antu da fasahar kirkire-kirkire.

Ya ce, idan ana duba matakin ci gaban kasa, to ya kamata a duba jimilar tattalin arzikin kasa da kuma adadin kudin shiga da kowanne 'dan kasa ke samu.

Duk da cewa ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kudin shigar da kowanne 'dan kasa ke samu a shekarar 2016, na matsayin kaso 80 na matsakaicin matakin a duniya, kuma 1 bisa 7 na Amurka, inda kuma ta zo na 68 a wannan fanni a duniya.

Sannan abun da kowanne 'dan kasa yake kashewa wajen sayen kayayyakin bukata shi ne dalar Amurka 2,506 a shekarar 2016, wanda bai kai rabin matsakaicin matakin na duniya ba, inda ya tsaya kan kaso 7 idan aka kwatanta da na Amurka.

Alkaluman kudin da ake kashewa kan sayen kayayyakin abinci idan aka kwatanta da kudin da ake kashewa kan sauran kayayyakin bukata na gida sun tsaya kan kaso 29.3 a kasar Sin, adadin da ya fi na kasashen da suka ci gaba yawa.

Ya ce, wannan na nufin har yanzu kasar Sin na kashe kudi masu yawa kan kayayyakin bukata, kuma kudin da al'ummar kasar ke kashewa kan abubuwan da suka shafi al'adu da kiwon lafiya da nishadi da yawon bude ido sun yi kasa sosai da wanda ake kashewa a kasashen da suka ci gaba.

Har ila yau, Wang ya ce akwai bukatar inganta tsarin masana'antu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China