in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kara bude kofarta ga kasashen waje
2016-12-15 11:16:01 cri

Yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar kwanakin baya ba da dadewa ba, game da aikin tattalin arziki na shekarar 2017, mahalarta taron sun jaddada cewa, zuba jari a kasashen ketare, da kuma shigo da jarin waje nan kasar Sin suna da muhimmanci kwarai, kana sun yi nuni da cewa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya", tare kuma da kara kyautata aikin gudanar da harkokin kasa bisa doka, domin kyautata muhallin zuba jari. Kwararrun da abin ya shafa suna ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta riga ta samu sabon ci gaba wajen bude kofarta ga kasashen waje. A shekara mai zuwa kuwa, za ta hanzartar tsara sabon tsarin tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba.

Kamfanin hada magunguna na Novartis, wani shahararren kamfanin hada magunguna ne da aka kafa a kasar Swiss. A watan Yunin bana, cibiyar nazarin da kamfanin ya kafa a yankin ciniki maras shinge na birnin Shanghai na kasar Sin ta fara aiki. Ta kuma kasance cibiyar nazari ta uku ta kamfanin tun bayan da aka kafa sauran cibiyoyin nazarinsa a Swiss da kuma Amurka. Daraktan kula da huldar waje ta kamfanin Wang Peng ya gaya mana cewa, gaskiya sun gano cewa, muhallin zuba jari na kasar Sin yana kara kyautatuwa a kai a kai. Wang Peng ya ce, "Cikin dogon lokaci, muna yin cudanya da kuma tattaunawa da hukumomin gwamnatin kasar Sin. Ana iya cewa, hukumomin gwamnatin birnin Shanghai sun samar da hidima mai inganci. Misali hukumar sa ido kan aikin shigar da kayayyakin gwaji daga kasashen waje ta kasar Sin, da hukumar kiwon lafiya da shirin haihuwa, da hukumar bincike, da kwastan, dukkansu suna yin kwaskwarima domin kyautata aikinsu, kuma sun samu sakamako a bayyane, har muna iya shigo da kayayyakin gwajin daga kasashen waje cikin wata guda kacal. Lallai hakan ya taimaka matuka ga aikinmu."

Bisa alkaluman da hukumar gwamnatin kasar Sin ta samar, an ce, a cikin watanni goma na farkon shekarar bana, adadin kamfanonin da aka kafa bisa jarin da 'yan kasuwar kasashen waje suka zuba ya kai dubu 22 da 580, adadin da ya karu da kaso 7.4 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara. Kana adadin jarin waje da aka yi amfani da shi, ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 666 da miliyan 300, adadin da ya karu da kaso 4.2 cikin dari, idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara. A bayyane take cewa, kasashen duniya suna da babbar sha'awa kan kasuwar kasar Sin. Ban da haka kuma, sakamakon binciken taron raya ciniki na MDD ya nuna cewa, a shekarar bana da muke ciki, da kuma shekara mai zuwa, kasar Sin tana sahun gaba a fadin duniya wajen shigo da jari daga kasashen ketare.

Kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Sun Jiwen ya bayyana cewa, "Tun daga farkon shekarar bana, shahararrun manyan kamfanoni na kasashe mambobin kungiyar kasashen Turai da yawansu ya kai 28 sun kara zuba jari a kasar Sin, musamman ma kan fasaha. Hakan ya nuna cewa, wadannan manyan kamfanonin suna cike da imani kan makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Kana suna cike da imani kan babbar kasuwar kasar Sin, wadda ke da yawan mutanen biliyan 1 da miliyan 370."

A halin da ake ciki yanzu, kwamitin kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin ya fitar da wata sabuwar takarda game da ba da jagoranci kan kamfanonin da 'yan kasuwar kasashen waje za su zuba jari cikin su, inda aka gano cewa, gwamnatin kasar Sin ta rage kayyadewar da take yi wa jarin waje bisa babban mataki.

Kwararriyar dake aiki a cibiyar nazarin huldar kasa da kasa ta zamani ta kasar Sin Chen Fengying ta bayyana cewa, hakan ya alamanta cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen shigo da jari daga ketare. Chen Fengying tana mai cewa, "Yanzu mun rage kayyadewar da ake yi wa jarin waje bisa babban mataki, inda ya zamo yana kumshe da fannoni 62 kacal, nan gaba kuma za mu ci gaba da yin kokari domin kyautata aikinmu."

Yanzu haka kasashe sama da 70 a fadin duniya, suna gudanar da manufar kayyade jarin waje, wato an tanadi cewa, a wasu harkokin kasashen, an hana 'yan kasuwar kasashen waje su zuba jari. A hannu guda kuma kasar Sin tana kokari a wannan fanni, musamman ma a yankin ciniki maras shinge da aka kafa a Shanghai da kuma Tianjin. Chen Fengying tana ganin cewa, sabuwar takardar da kasar Sin ta fitar za ta sa kaimi kan aikin bude kofa ga kasashen waje, haka kuma za ta sa kaimi kan jarin waje da ake shigowa da shi daga kasashen waje, da ya kara taka rawa kan ci gaban tattalin arziki a kasar Sin.

A yayin taron hukumar siyasar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar a kwanakin baya, an sake jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da kara shigo da jarin waje a shekarar 2017 dake tafe. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin samar da wani muhalli na gari ga 'yan kasuwar kasashen waje domin kara zuba jari a kasar ta Sin. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China