in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin bude kofa na kasar Sin ya samarwa nahiyar Afrika wata hanya ta samun cigaban harkokin zamani
2018-03-12 10:48:48 cri
An bayyana tsarin bude kofa na kasar Sin cikin shekaru 40 da suka gabata a matsayin wata sabuwar hanya ta samun ci gaban harkokin zamani ga nahiyar Afrika.

Wata kwararriya kan harkokin tattalin arziki Anzetse Were ce ta bayyana haka yayin da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Juma'a, inda ta ce wasu kasashen Afrika sun amfana sosai daga tsarin kasar Sin na bude kofa ga kasashen waje.

Ta ce abu mafi muhimmanci shi ne, yadda tsarin ya nunawa kasashen Afrika cewa, bunkasuwar masana'antu su ne jigon samun ci gaba kuma za a iya aiwatar da su ta mabambamtan hanyoyi.

Ta bada misali da kasashen Rwanda da Habasha, inda ta ce kasashen biyu na gabashin Afrika da suke bin tafarkin neman ci gaba irin na kasar Sin, sun samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri fiye da sauran yankin, inda a shekarar 2016, Rwanda ta samu karin kaso 5.9, yayin da Habasha ta samu kaso 8.0.

Kwararriyar wadda 'yar asalin kasar Kenya ce, ta ce kasar Sin ta cancanci yabo bisa managartan dabarunta na kasuwanci, inda ta ce akwai abubuwa da dama da kasashen Afrika za su iya koyo daga gare ta.

Har ila yau, ta ce kamata ya yi masana'antu a Afrika su fara sarrafa albarkatun da nahiyar ke da su wajen samar da kayayyaki ga jama'arta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China