Firaministan Sin Li Keqiang ya halarci taron, tare da gabatar da jawabi mai lakabi "kirkiro da sabbin tunani don kawo kuzari ga raya Asiya".
Sakatare janar na dandalin Zhou Wenzhong a jawabin shi ya ce, an mai da hankali game da hada-hadar kudi ta shafin Internet da more tattalin arziki, da yin gyare-gyare kan tsarin samar da kaya, da na'urori masu amfani da fasahar kansu da tattara kudade, baki daga sassan daban daban sun tattauna game da wadannan batutuwa, kuma sun lalubo bakin zaren warware batutuwan, don kawo kuzari ga raya tattalin arziki a Asiya.
Zhou Wenzhong ya ce, a yayin taron, masanan tattalin arziki da 'yan kasuwa sun cimma matsaya guda, wato wanda ya zama dole a yi gyare-gyare game da tsarin samar da kayayyaki, don raya tattalin arzikin Asiya. Wakilai mahalartar taron sun dora muhimmanci game da batun yi gyare-gyare game da tsarin samar da kayayyaki da kasar Sin ke gudanarwa, wasu da dama suna ganin cewa, kamata ya yi a hada aikin samar da kayayyaki da na bukatu tare.(Bako)