in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kalubalanci matakin Amurka na kara haraji, kuma za ta dau fansa
2018-04-04 09:56:32 cri
A yau Laraba ma'aikatar cikinin kasar Sin (MOC) ta sanar da cewa kasar tana adawa da matakin Amurka na yunkurin kara kudaden haraji, kana ita ma za ta dauki fansa a kan kayayyakin da Amurka ke kerawa.

Kakakin ma'aikatar ta MOC ya bayyana hakan ne bayan da gwamnatin Amurka ta sanar da aniyarta na kara kudaden haraji a jerin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurkar, wanda adadin kudin ya kai dalar Amurka biliyan 50 wato kwatankwacin karin harajin na kashi 25 bisa 100 ke nan.

Dangane da nuna rashin amincewar da kasar Sin din ta nuna, matakin da Amurkar ta dauka na kara harajin al'amari ne marar tushe balle makama, wanda kuma mataki ne da Amurkar ta dauka bisa son zuciyarta wanda kasar Sin tayi Allah wadai da shi, kamar yadda sanarwar ta tabbatar da hakan.

Wannan mataki dai zai iya kawo illa ga moriyar kasar Sin, da Amurkar har ma da tattalin arzikin duniya, kuma ya sabawa ka'idojin hukumar ciniki ta duniya (WTO).

Kasar Sin tana kokarin hanzarta gabatar da wannan batun ga sashen warware sabani na hukumar WTO, kuma a shirye take da dauki fansa a kan kayayyakin da Amurkar ke samarwa wanda yayi daidai da irin matakin da Amurkar ta dauka, kuma nan da wasu kwanaki masu zuwa Sin zata tabbatar da hakan.

Kakakin ma'aikatar cinikin ta Sin ya kara da cewa, kasar Sin tana da kwarin gwiwa da kuma damar da za ta ita maidawa Amurkar martani kan huldar cinikayya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang shi ma ya mayar da makamancin wannan martani a yau Laraba, yana mai cewa, matakin karin harajin da Amurkar ta dauka ta yi hakan ne bisa radin kanta kuma a shirye kasar Sin take ta kare kanta.

Duk da irin gargadin da kungiyoyin 'yan kasuwa da masana harkokin ciniki na kasa da kasa ke yi , shugaban Amurka Donald Trump ya yi kunne kashi wajen sanya hannu kan yarjejeniyar kara kudin harajin a ranar 22 ga watan Maris kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China