in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwanci ta Sin ta amsa tambayoyi game da batun kara sanya haraji kan kayayyayin da take shigowa daga kasar Amurka
2018-04-02 13:49:28 cri
Game da yadda kasar Sin ta yanke shawarar kara sanya haraji kan wasu kayayyakin da take shigar dasu daga kasar Amurka, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar a yau Litinin ya bayyana cewa, ana fatan kasar Amurka zata soke matakan da suka sabawa ka'idojin hukumar cinikayya ta duniya wato WTO cikin hanzari don magance kara kawo illa ga yanayin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka.

Kakakin ya bayyana cewa, Sin ta dakatar da wasu ayyuka na baiwa kasar Amurka gatanci a cinikayyar da ke tsakaninsu, shi dai hakkin kasar Sin a matsayin memban hukumar WTO ne. A ranar 26 ga watan Maris ne, kasar Sin ta gabatar da bukatun yin shawarwari da kasar Amurka game da matakan ban gishiri in ba ka manda bisa yarjejeniyar matakan bada tabbaci ga ciniki, amma kasar Amurka taki amincewa. Sakamakon gaza cimma daidaito a tsakaninsu, Sin ta gabatar da jerin kayayyayin da take shigowa daga Amurka wadanda za ta dakatar da rangwame a kansu ga hukumar WTO, inda ta tsaida kudurin kara haraji kan kayayyakin don daidaita hasarorin da aka samu yayin da kasar Amurka ta dauki matakin mai lamba 232.

Kakakin ya kara da cewa, a matsayin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, ya kamata Sin da Amurka su yi hadin gwiwa, da warware matsalolin ta hanyar yin shawarwari, da samun bunkasuwa tare don magance kara kawo illa ga yanayin hadin gwiwarsu a nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China