in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta yi hasashen karuwar ciniki a duniya zai kai kasha 2.4% a bana
2017-04-13 13:23:08 cri
Hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO, ta yi hasashen cewa, harkokin ciniki tsakanin kasa da kasa zai karu da kashi 2.4% a bana.

Cikin rahoton da hukumar ta fitar a jiya, babban darektanta Roberto Azevedo, ya yi bayanin cewa, idan masu tsara manufofi sun dauki tsauraran matakai na kayyade shigar da kayayyaki domin samar da guraben aikin yi a kasashensu, lallai harkokin cinikayya ba za su taimakawa bunkasar tattalin arziki ba, inda ya ce zai iya yi wa farfadowar tattalin arziki tarnaki.

A don haka, ya yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa, da su inganta aikin samar da ilimi da bada horo, don yin amfani da harkokin cinikayya wajen kara samar da guraben aikin yi. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China