in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron WTO a Argentina
2017-12-11 15:51:00 cri
An bude taron hukumar kula da harkokin kasuwanci ta duniya WTO jiya Lahadi a birnin Beunos Aires na Argentina, inda aka jadadda muhimmancin bude kofa da cinikayya tsakanin kasa da kasa.

A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na hukumar Roberto Azevedo, ya ce kara bude kofa da saukaka hanyoyin cinikayya za su kara bada dimbin damarmakin cimma nasara.

A nasa jawabin, shugaban Argentina Mauricio Macri, kira ya yi ga mambobin hukumar su inganata tsarin tabbatar da adalci da kasuwancin tsakanin kasa da kasa da bisa ka'idoji masu sauki.

Taron wanda zai kai har Laraba ana yinsa, zai hada jami' an harkokin cinikayya daga kasashe mambobin hukumar 164, inda za su tattauna kan yadda za a yi inganta ka'idojin cinikayya a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China