in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta ce a shirye take tattauna da Amurka don ganin an cire ta daga jerin 'yan ta'adda
2018-03-19 09:19:54 cri

Kasar Sudan ta ce a shirye take ta koma tattaunawa da Amurka domin ganin an cire ta daga jerin sunayen 'yan ta'adda na Amurka.

Cibiyar yada labarai ta kasar ta ruwaito ministan harkokin wajen kasar Mohammed Abdallah Idris na cewa, a shirye gwamnatin kasar take ta fara zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka domin cire sunan Sudan daga jerin kasashen dake daukar nauyin 'yan ta'addanci.

Duk da cewa bai fadi ranar da za a yi tattaunawar ba, ya ce gwamnati na aiki don ganin ta kammala tattaunawa da Amurka kamar yadda aka tsara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China