in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka za ta iya warware rikicin Sudan ta kudu, in ji jakadan Sin
2018-02-06 10:12:54 cri

Jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu He Xiangdong, ya ce kasashen Afirka na da zarafi na kawo karshen tashin hankalin dake addabar Sudan ta Kudu, ta hanyar amfani da dabaru masu tasiri ga nahiyar.

He Xiangdong wanda ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, a gefen bikin bude taron kungiyar shugabannin kasashen gabashin Afirka ta IGAD a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya ce duk da sarkakiyar da yanayin Sudan ta kudu ke da shi, ya yi imanin kasashen nahiyar Afirka za su iya shawo kan matsalar yadda ya kamata.

Ya ce, duba da cewa Sudan ta kudu daya ce daga kasashe mambobin kungiyar IGAD 8, akwai fatan kungiyar da ma sauran kasashen Afirka za su yi hadin gwiwa wajen warware matsalar kasar, musamman kasancewar makomar nahiyar na hannu su.

Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar Sin, na ci gaba da goyon bayan dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki wajen warware danbarwar siyasar Sudan ta kudu, ciki hadda kasashe mambobin kungiyar ta IGAD da kungiyar AU.

Sudan ta kudu dai ta shafe shekaru sama da 4 tana fama da tashe tashen hankula da ke jawo asarar rayukan jama'ar ta, lamarin da ya haifar da gagarumar matsalar 'yan gudun hijira da ake ci gaba da fuskanta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China