in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan za ta bude kofar zuba jari a bangaren hakar sinadarin Uranium
2018-03-13 10:15:25 cri

Ministan ciniki na kasar Sudan Hatim al-Sir, ya ce gwamnatin kasar ta yanke shawarar bude kofa ga masu zuba jari a bangaren hakar sinadarin Uranium.

Hatim al-Sir wanda ya bayyana haka a jiya, ya ce ya gana da shugaba Omar al-Bashir game da batun bude kofa ga masu zuba jari a bangaren hakar Uranium bayan ya tuntubi hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa, yayin ganawar, sun kuma amince da yi wa dokokin cinikayya da na hada-hadar kudaden ketare gyaran fuska, musammam ma dokar da ta shafi sinadaran karkashin kasa, wadda ta haramta fasa kauri da adanawa da fitar da albarkatu masu daraja zuwa kasuwannin ketare a kan farashi kasa da wanda aka kayyade.

A watan Yulin shekarar 2015 ne hukumar binciken kasa ta Sudan, ta ce za a ba kamfanonin kasar Rasha damar bincike da hako sinadarin Uranium, la'akari da fasahohin zamani da kasar ke da su.

Hukumar ta ce Sudan ita za ta iya hakar Uranium, saboda an gano adadi mai yawa na sinadarin a sassa daban-daban na kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China