Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin, inda ya kara da cewa, kasarsa na fatan ganin bangarori daban daban da batun ya shafa sun hada kai don inganta kyautatuwar dangantaka a tsakanin kasashen Koriya ta arewa da ta kudu, kana tana fatan Koriya ta arewa da Amurka za su samu ci gaba da yin shawarwari. (Bilkisu)