in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron dandalin tattaunawar kare hakkin bil Adam a birnin Beijing
2015-09-17 19:28:55 cri
A yau Alhamis ne aka rufe taron dandalin tattaunawar kare hakkin bil Adam na shekarar 2015 da cibiyar nazarin kare hakkin bil Adam ta kasar Sin da asusun kare hakkin bil Adam na kasar Sin suka shirya a nan birnin Beijing.

Taken taron a wannan karo shi ne "zaman lafiya da bunkasuwa, nasara kan yaki da masu nuna ra'ayin karfin tuwo a duniya da ci gaban kare hakkin bil Adam", inda a cikin kwanaki biyu na taron, manyan jami'an kula da harkokin kare hakkin bil Adam da masana sama da 100 da suka fito daga kasashe fiye da 30 suka yi musayar ra'ayoyi a kan batun.

Mahalarta taron suna ganin cewa, a yayin da ake murnar cika shekaru 70 da Sinawa suka samu nasara a kan maharan kasar Japan da kuma nasarar yaki da masu ra'ayin nuna karfi a duniya baki daya, taron da aka yi game da nuna kyamar yaki da kare hakkin bil Adam da kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da bunkasa harkokin kare hakkin bil Adam a duniya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China