Masana daga cibiyar nazarin harkokin teku karkashin cibiyar nazarin kimiya ta kasar Sin sun bayyana cewa, binciken da suka gudanar a yammacin tekun Fasifik a karshen shekarar da ta gabata ya tabbatar da tsawon kwanakin da masanan suka shafe a wuri mai zurfi na teku, bayan da suka inganta tsarin sadarwar tattara bayanai.
Daya daga cikin masanan na kasar Wang ya bayyana cewa, lokacin da masanan suka kwashe a yankin teku mai zurfi, ya samar da muhimman bayanai ga bincike masu sarkakiya da ake gudanarwa game da yanayin teku da na duniya. Yana mai cewa, muhimman bayanan za su kara inganta sahihancin hasashen da ake yi game da yanayin teku da na muhalli.
A cewar cibiyar kambun gajin nutsu a yankin teku mai zurfi da ya gabata dai shi ne kwanaki 90. (Ibrahim)